(ABNA24.com) A cikin jawabin da ya gabatar wa jama’ar ‘yan kasar da yammacin jiya, Shugaba Sall, ya sanar daukan wasu matakai na sassauta matakan da aka dauka a ranar 23 ga watan Maris da ya gabata domin dakile yaduwar annobar.
Daga cikin matakan da zasu fara aiki daga yau Talata har da sassauta dokar hana zirga zirga dare zuwa karfe 08:00 na dare zuwa 06:00 na safe, maimakon 09:00 zuwa 05:00 na safe.
Saidai shugaban kasar ya ce gwamnati za ta sanya ido sosai akan ganin an kiyaye matakan kare kai daga cutar, irinsu takunkumin rufe fuska da kuma nisantar juna a wuraren ibada, makarantu, wuraren dake fuskantar cinkoson jama’a da kasuwanni da kuma wuraren cin abinci.
Haka kuma a cewar shugaba Macky Sall, kasar za ta fara maido gawarwakin mutanenta da suka rasu a kasashen ketare.
A halin da ake dai mutane 1,886 ne suka harbu da cutar korona a Senegal, sai kuma 19 da cutar ta kashe.
/129
13 Mayu 2020 - 06:20
Lambar labari: 1036345
Shugaban kasar Senegal, Macky Sall, ya sanar da sassauta matakan da kasarsa ta dauka na yaki da cutar Korona.